
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya nanata cewa dole jam’iyyar PDP ta tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya a shekarar 2027.
Wike ya bayyana hakane a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da ya gudana ranar Litinin a Abuja.
An gudanar da taronne dan warware matsalar dake tattare da jam’iyyar da kuma saitawa jam’iyyar Alkibla.
Wike yayi gargadin cewa jam’iyyar PDP ta kama hanyar kashe kanta inda yace idan ba’a gyara ba aka ajiye jiji da kai da son rai ba, abinda ya faru a jam’iyyar a shekarar 2023 zai sake maimaita kansa.
Yace kuma idan ana son Adalci da amfani da tsarin raba daidai da tsarin mulkin jam’iyyar PDP, dole a tsayar da dan takara daga kudancin Najeriya a jam’iyyar ta PDP.