
A jiyane, babbar kotun tarayya dake Abuja ta yi hukuncin cewa a mayar da Sanata Natasha Akpoti cikin majalisar Dattijai a janye dakatarwar da aka mata.
Saidai a martanin majalisar ta bakin me magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu ya bayyana cewa, majalisar ba zata yi gaggawar dawo da sanata Natasha Akpoti bakin aiki ba.
Yace majalisar zata yi zama tukuna kamin ta yanke hukuncin da zata dauka kan dawo da Sanata Natasha Akpoti.
Ya kara da cewa, kotun bata hana majalisar Dattijai hukunta membobinta ba dan haka sai sun yi zama kamin sanin matakin da ya kamata su dauka.