
Kungiyar kwadago ta NLC ta yi gargadin cewa idan aka ce za’a kara kudin wutar lantarki ba zasu amince da hakan ba, zasu tafi yajin aiki.
Kungiyar tace ba zata amince da duk wata dabara ta kokarin kara kudin wutar lantarkin ba.
Tace idan aka yi hakan zata jagoranci gagarumar zanga-zanga.
Kungiyar ta NLC tace tana sane da shirin da ake yi na mayar da kowa da kowa kan tsarin Band A na wuta da sunan wai inganta samar da wutar, kungiyar tace ba zata amince da hakan ba dan yunkuri ne na kara kudin wutar lantarkin.