
Rahotanni daga kasar Canada inda aka yi taron kasashe 7 mafiya karfin tattalin Arziki wadanda ake kira da G7 sun bayyana cewa, ba zasu amince kasar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba.
Kasashen sun ce suna son a samu zaman lafiya a gabas ta tsakiya kuma sun amince kasar Israyla na da damar kare kanta.
Sun bayyana cewa kasar Iran itace ummul aba isin rashin zaman lafiyar da ake fama dashi a yankin na gabas ta tsakiya.
Dan haka suna jaddada matsayarsu ta cewa ba zasu amince kasar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba.
Kasashen G7 da shuwagabannin su sune kamar haka:
Donald J Trump (The USA)
Keir Starmer (The UK)
Friedrich Merz (German Chancellor)
Giorgia Meloni (Italy PM)
Emmanuel Macron (France)
Shigeru Ishiba (Japan PM)
Wasu kasashen Duniya da aka gayyata zuwa wannan taro sun hada da Australia, South Korea, Brazil, India, Mexico, Ukraine da South Africa