
Shugaban kotun shari’ar Musulunci dake jihar Kwara, Justice Abdurraheem Sayi ya bayyana cew basa bukatar amincewar hukumin Gwamnati ko na sarakunan gargajiya kamin su kafa kotun shari’ar Musulunci.
Yace duk masu adawa da kafa kotunan shari’ar musulunci a jihohin Yarbawa kiyayyar addinin ce kawai ta sasu hakan ba wani abuba.
Ya bayyana hakane a yayin da yake gabatar da yawabi a jami’ar Legas akan maganar shari’ar Musulunci a jihohin Yarbawa.
Ya bayyana cewa ko shugaban kasa, doka bata bashi damar hana samar da kotun shari’ar Musulunci ba.
Yayi kira ga mahukunta a yankin dasu bayar da dama ga musulman dake so su aiwatar da shari’ar Musulunci domin dokokin jihohinsu basu baiwa musulmai irin wannan dama ba.