Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka, Rihanna ta bayyana cewa, abinda take Alfahari dashi a shekarar 2024 shine har shekarar ta fara ta kare bata sha giya ko sau daya ba.
Rihanna dai ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta yayin da take murnar shigar sabuwar shekara.
A kwanaki dai Rihana ta bayyana cewa ta yi nadamar shigar tsiraici da ta rika yi a baya inda tace babban abinda ya sata nadama shine da ta ga ta zama uwa.