Wednesday, January 15
Shadow

Babbar Sallah: Gwamnatin jihar Sokoto ta amince a biya albashin watan Yuni

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya albashin watan Yuni ga ma’aikatan jihar daga ranar Litinin.

Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma’aikatan gwamnatin jihar damar yin bikin babbar sallah cikin walwala.

Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce dukkan ma’aikatan jihar, da na ƙananan hukumomi da kuma ƴan fansho ne za su amfana da wannan karamci.

Abubakar Bawa, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da biyan albashin ma’aikata a kan lokaci, kamar yadda ya ce ya zama al’adar gwamantin, biyan albashi a ranar 20 zuwa 21 na kowanne wata, tun bayan karɓar ragamar mulki.

Karanta Wannan  A yayin da shuwagabanni da 'yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

Dama dai gwamnonin jihohin Arewa sun saba yin irin wannan karamci idan aka samu yanayi na gudanar da shagulgulan sallah amma wata bai ƙare ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *