
Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa babu dan Arewar da ya isa ya zama shugaban kasa sai a shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gama wa’adinsa karo na biyu.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja.
Wike yace dan Arewa ya yi mulki har sau biyu dan haka Shima Tinubu sai yayi sau biyu daga kudu kamin wani dan Arewa ya sake mulka.
Yace babu wani yanki da zaice shi kadai zai ta yin mulkin Najeriya, tsarin karba-karba za’a ci gaba da yi.