Thursday, April 30
Shadow

Babu Dan Arewa da ya isa ya zama shugaban kasa a 2027 sai 2031 bayan Tinubu ya gama saboda Buhari ma sau biyu yayi mulki>>Inji Wike

Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa babu dan Arewar da ya isa ya zama shugaban kasa sai a shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gama wa’adinsa karo na biyu.

Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja.

Wike yace dan Arewa ya yi mulki har sau biyu dan haka Shima Tinubu sai yayi sau biyu daga kudu kamin wani dan Arewa ya sake mulka.

Yace babu wani yanki da zaice shi kadai zai ta yin mulkin Najeriya, tsarin karba-karba za’a ci gaba da yi.

Karanta Wannan  Majalisar mu ta dattijai kamar kungiyar tsafi take, kowane Sanata na tsoron ya soki kakakin majalisa, Akpabio ya taba rike min hannu ya rika murzawa, kowace mace akawa haka tasan abinda ake nufi>>Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Akpabio tonon silili

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *