
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa, babu irin muguntar da tsohuwar gwamnatin APC batawa Tinubu ba dan kada ya zama shugaban kasa ba amma Allah ya tsallakar dashi.
Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.
Yace An kawo sabbin tsare-tsare na wahalar man fetur da canjin kudi da sauransu duk dan a hana Tinubu zama shugaban kasa amma Allah ya tsallakar dashi.
Yace haka ne ke faruwa dama idan Allah na son mutum.
Yace kuma babu maganar wani dan Arewa ya sake zama shugaban kasa a Najeriya har sai bayan shekarar 2031 bayan Tinubu ya kammala mulkinsa zango na biyu.