
Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA ta fitar da matsaya game da auren ‘YarGuda da Maiwushirya.
Kungiyar tace ta samu labarin auren wanda wata kotun Magistrate ta yi a Kano.
Tace babu wata kotu dake da hurumin tursasa mutum yayi aure saboda hakan take hakkin bil’adama ne saboda aure abune wanda mutum ke yi saboda akwai soyayya da fahimtar juna tsakanin masoyan.
Dan haka NBA tace tana neman a sake duba wannan hukunci dan tabbatar ba’a takewa wanda lamarin ya shafa ba hakkinsu.
Saidai Rahotanni sun nuna cewa, Maiwushirya da kanshi ne yace zai auri ‘YarGuda inda itama ta amince da hakan.