
,Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a bayyana cewa, babu shugaban da zai cimma Nasara ba tare da rufe ido da murza gashin baki ba da yin abinda ya dace.
Ya bayyana hakane a yayin da sabon shugaban ma’aikatar lafiya ta tarayya dake Idi-Aba, Abeokuta, Dr. Dayo Israel ya kai masa ziyara.
Tsohon shugaban kasar ya bayar da misali da kansa inda yace ya taba ya taba korar diyarsa daga aiki a gonarsa sabod ta je aiki a makare.
Ya jaddada cewa muddin shugaba na son cimma nasara sai ya fuskanci kalubalen dake gabansa da gaske.