
Tsohon sanatan kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya mayarwa da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai martani kan maganar da yayi cewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu baya son yin aiki dashi.
A hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Arise TV, El-Rufai ya bayyana cewa ba majalisa bace ta ki amincewa dashi a matsayin minista ba, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya fasa bashi mukamin duk da cewa sun yi alkawari akan hakan.
Saidai a wani matsayi na martani ga El-Rufai, Sanata Shehu Sani ya rubuta a shafinsa cewa, Babu shugaban kasa yanzu ko nan gaba dake cikin hayyacinsa zai jawo mutumin da yayi alfahari da aika tsohon shugaban kasa, Umar Musa ‘Yar’adua zuwa Kabari.
Sanata Sani ya kara da cewa, ai mutum zai yi tunani cewa tunda kawa dan uwanka haka, to lallai bima zaka iya min.
Sanata Shehu sani dai wanda suka dade suna tsama da Nasor El-Rufai tun bayan da ya hana El-Rufai cin Bashi lokacin yana Sanata Shi kuma El-Rufai yana gwamna bai kira suna ba, amma duka alamu sun bayyana cewa da El-Rufai yake.
Dalili kuwa shine a likacin da yake Gwamna, Nasir El-Rufai da yake fadar cewa fada dashi ba riba, ya taba bayar da misalin wanda suka yi fada dashi basu samu nasara ba, watau Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan wanda yace ya koma Otueke( watau bai sake cin zabe ba) inda ya karasa da cewa dayan kuma yana kabari, watau Marigayi, tsohon shugaban kasa, Umar Musa ‘Yar’adua.