
Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta Najeriya Nafdac ta ce ta rufe sama da shaguna 11,000 tare da kama mutum 40 a yaƙin da take yi da sayar da ƙwayoyin jabu.
Da take yi wa ‘yanjarida jawabi a ranar Lahadi, shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce sun tsara samamen ne tun shekara ɗaya da ta wuce.
Zuwa yanzu, Nafdac ta kai samame kasuwanni da dama ciki har da Idumota a Legas, da Ariaria a garin Aba, da Bridge Market a Onitsha a ranar 10 ga watan Fabrairu.
Ta ce sun hari kasuwanni uku da ke rarraba kashi 80 cikin 100 na magunguna a Najeriya, kuma sun yi nasarar kamawa tare da ƙwace ƙwayoyin jabu da waɗanda ba a yi wa rajista ba.
Farfesar ta kuma sun samu sama da mota 20 ta jabun magunguna a Aba, aƙalla 30 a Onitsha, da wasu 27 a kasuwar Idumota.
“Abin da muka sa a gaba yanzu shi ne fara duba ɗaiɗikun shaguna domin gano masu karya doka da kuma waɗanda ba su da rajista,” in ji ta.