
Tsoho gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa dan Abba ya koma jam’iyyar APC bai ga wani abin Butulci ba.
Yace watakila Kwankwaso ya manta amma idan shi ya manta, mutane basu manta ba, yace shima Kwankwason ya canja jam’iyyu.
Yace tare suka shiga jam’iyyar NNPP da su Kwankwaso amma rashin Adalci wajan rabon mukamai yasa suka fita dsga jam’iyyar.
Yace yawanci dan siyasa na canja jam’iyya ne bayan ya ssmu goyon bayan mabiyansa dan haka bai ga abin ace Abba yawa wani Butulci ba.