
Wani limamin masallaci a kasar Afrika ta Kudu me suna Moegsien Hendricks ya bakunci lahira bayan da ya yi yunkurin daura auren jinsi.
Limamin wanda ya riga ya fito ya bayyanawa Duniya cewa shi dan luwadine ya shahara sosai.
Wata yarinya ce wadda itama musulmace amma take son auren ‘yar uwarta mace dan yin madigo ta gayyaceshi ya daura mata aure da wadda take so wadda ba musulma bace.
An kasheshi ne a garin Bethelsdorp a ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu yayin da ya kai inda zai daura auren.
Kakakin ‘yansanda na birnin, Captain Sandra Janse van Rensburg ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace mutane biyu ne fuskokinsu a rufe suka je da mota kirar Hilux suka kashe limamin.
Ta kara da cewa, ba’asan manufarsu ta aikata hakan ba inda tace duk wanda ke da bayani akan maharan ya kawo musu tsegumi.
Shi dai wannan malami har kungiya ya bude wai da sunan taimakawa musulmai ‘yan luwadi da madigo da sauran masha’a.