Wednesday, May 7
Shadow

Bakar fata dan kasar Ghana na cikin na gaba-gaba da ake tunanin zasu gaji Fafaroma

Idan dai ana duba bunƙasar cocin Katolika ne wajen zaɓen fafaroma na gaba, da tabbas babu wani zaɓi illa daga Afirka.

Afirka ce ke da mabiya Katolika da suka fi ƙaruwa cikin sauri a duniya, inda suka ƙaru da kashi 3.31 cikin 100 a shekara biyu tsakanin 2022 da 2023. Alƙaluma na baya-bayan nan daga Fadar Vatican kashi 20 na mabiya Katolika ne ke zaune a Afirka.

A gefe guda kuma, nahiyar Turai ta fuskanci ƙaruwa mafi ƙanƙanta a wannan lokaci. Daga shekarar 1910 zuwa 2010, an samu raguwar mabiya ɗariƙar da sama da kashi 63, a cewar alƙaluman binicke na cibiyar Pew Research.

Nahiyar ta Turai da ake yi wa kallon cibiyar Kiristanci ta duniya, yanzu ta zama ɗaya daga cikin mafiya nisa da addini gaba ɗaya.

Duk da cewa har yanzu Katolika na da ƙarfi a nahiyar Latin Amurka, Ibanjilika na ƙwace mata mabiya a ƙasashe da dama. Wani bincike da cibiyar Latinobarómetro ta gudanar a ƙasashe 18 na nahiyar ya gano mutanen da ke kiran kan su ‘yan Katolika sun ragu da kashe 70 cikin 100 zuwa kashi 57 a 2020.

Saboda haka idan cardinal suka taru domin zaɓen sabon fafaroma a Fadar Vatican, ko za su mayar da hankali kan wurin da mutum ya fito kafin yanke hukuncin?

Fada Stan Chu Ilo, wani mai wa’azin Katolika ne a Najeriya, kuma yana ganin za su yi hakan.

Karanta Wannan  Farashin Man fetur ya sauka

“Ina ganin zai yi kyau a samu fafaroma ɗan Afirka,” a cewarsa, yana mai nuna cewa ya kamata a ce shugabancin cocin ya nuna alamun yawan mabiyanta a duniya.

Fafaroma Francis ne ya ƙara yawan cardinal ɗin da ake naɗawa daga ƙasashen Afirka baƙar fata, waɗanda za su zaɓi wanda magajinsa daga kashi 9 cikin 100 lokacin da aka zaɓe shi a 2013 zuwa kashi 12 a 2022. Amma Fr Chu Ilo ya ce hakan ba ya nufin lallai za su zaɓi ɗan Afirka.

Ya ce akwai yiwuwar cardinals ɗin za su zaɓi yake da dama sunansa ya shahara.

“Ƙalubalen shi ne, babu wani babba ɗan Afirka da ke riƙe da wani muhimmin muƙami yanzu a Vatican.

“Idan ka duba cardinals daga Afirka da ke da damar zama fafaroma, wane ne ke da wani tasiri a duniya a yanzu? Amsar ita ce babu.”

A cewar Chu Ilo, yanzu ba kamar 2013 ba ne lokacin da ɗan Ghana Peter Turkson ke da ƙarfin neman muƙamin, da kuma 2005 lokacin da ɗan Najeriya cardinal Francis Arinze ke da ƙarfi.

‘Kamar kyauta’

Yayin da aka taɓa yin fafaroma har uku daga Afirka , na ƙarshe da aka yi – Fafaroma Gelasius I – ya mutu ne tun shekara 1,500 da suka wuce. Mutane da dama na ganin lokaci ya yi da za a sake yin wani.

Karanta Wannan  Saudiyya ta saka tarar riyal 20,000 ga masu yin aikin Hajji ba bisa ƙa'ida ba

Sai dai wasu cardinals daga Afirka na gani nana yawan mayar da hankali kan wuraren da fafaroma suka fito. Kamar Fada Paulinus Ikechukwu Odozor, wani farfesa a jami’ar Notre Dame University kuma ɗan Najeriya mai wa’azin Katolika.

“Bai kamata a ce kawai don mutum ya fito daga Afirka ko Turai ba kawia shikenan ya zama ɗantakarar zama fafaroma,” in ji shi.

“Duk da inda mutum ya fito, da zarar an zaɓe shi, matsalolin kowa sun zama naka. Matsala ɗaya kawai mutum yake da ita, it ace gina mabiya Yesu duk a inda suke, duk yawansu, a kowane irin yanayi.”

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, in ji shi, kawai fafaroma ya zama babban jagoran cocin”.

Fada Odozor ya ce tambayar da ake yi masa game da ko ya dace a samu sabon fafaroma daga Afirka a matsayin “abin takaici saboda yadda ake nuna kamar wani lada ce”.

“Kamar mutane na cewa ne, ‘To tun da ‘yan Afirka mabiya Katolika na ƙaruwa, a ba su muƙamin fafaroma.'”

Yana ganin akwai buƙatar a ɗauki ƙarin matakai domin kare mabiya ɗariƙar ‘yan Afirka a fadar Vatican.

Wariyar launin fata a coci?

Kamar Chu Ilo, shi ma yana ganin duk da ƙaruwar yawan cardinals daga Afirka, ba su da iko mai yawa a cocin na Katolika.

“Ba wai ƙasƙantar da cardinals ɗin da Francis ya naɗa nake yi ba, amma idan aka naɗa su ana ba su iko? Ka bai wa mutanen da ka naɗa ƙarfin iko, ka amince musu game da aikin kuma ka ƙyale su s yi shi,” kamar yadda ya bayyana.

Karanta Wannan  Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Chu Ilo da Odozor sun koka kan abin da ka iya daƙile yunƙurin Fafaroma Francis wajen yunƙurin damawa da kowa a cocin.

“Irin wannan yanayin zai iya kawo wa fafaroma cikas duk irin tsantseninsa, saboda za a dinga kallonsa ne kawai a matsayin fafaroman Afirka.”

Zuwa ƙarshen 2022, Fafaroma Francis ya ɗauki biyu cikin uku na cardinals ɗin da za su zaɓi magajinsa. Hakan na nufin, dakwai yiwuwar duk wanda za a zaɓa zai kasance mai irin aƙidar Francis ta kula da talakawa da marasa ƙarfi.

Abin mamaki

Akwai wani dalili babba da zai hana a yi hasashen mutumin da zai maye gurbin Fafaroma Francis, in ji Chu Ilo.

“Mabiya Katoliak sun yi imanin cewa Allah da ruhi mai tsarki na taimakawa wajen zaɓar shugabannin cocin,” a cewarsa.

Kenan akwai yiwuwar ba da mamaki, kamar a 2013 lokacin da aka zaɓi Fafaroma Francis. “Ba shi mutane suka dinga hasaashe ba,” a cewar Chu Ilo.

A cewarsa: “Ina addu’ar Allah ya ba mu fafaroman da zai ci gaba da aiki irin na Francis, kuma zan yi fatan mutumin ya fito daga Afirka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *