
Majalisar Dattijai ta Najeriya tace bata amince da kirkirar sabbin jihohi ba.
Kakakin Majalisar, Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan.
Hakan na zuwane bayan da labarai a kafafen sada zumunta suka yadu cewa majalisar ta amince da kirkirar sabbin jihohi.
Sanata Senator Abdul Ningi ne ya kai maganar majalisar inda Akpabio yace tabbas an gabatar musu da neman kirkira jihohi 42 amma basu amince da maganar ba tukuna.
Akpabio yace mutane su rika bin labaran da majalisar kadai ta wallafa sahohai.