Friday, December 5
Shadow

Bamu da hannu a harin da kasar Israyla ta kawo muku, kada ku tabamu>>Amurka ta gayawa Ìràn

Kasar Amurka ta gayawa Iran cewa, kasar Israyla bata nemi shawarar ta ba kamin afka mata da yaki.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Amurka tace bata taimaki kasar Israyla ba ko bayar da hadin kai wajan harin da ta kaiwa kasar ta Iran ba.

Yace dan haka Iran kada ta taba sojojin kasar Amurka ko gine-ginen ta dake yankin na gabaa ta tsakiya.

Yace kasar Israela tace ta dauki wannan mataki ne dan kare kanta.

Yace aikinsu shine sh baiwa sojojinsu kariya.

Kasar Israyla tace gurare 12 ne ta kaiwa hari a kasar Iran ciki hadda tashar Nukiliyar ta.

Karanta Wannan  Hotuna: Kasar Libya ta kulle 'yan kwallon Najeriya a filin jirgi ta hanasu zuwa ko ina

Kasar Amurka ta baiwa mutanen ta musamman na ofishin jakadancin ta umarnin su yi ta kansu, ko su shiga maboya me bayar da kariya ga bom dan a ko da yaushe kasar Iran zata iya kawo harin ramuwar gayya wanda ba zai yi kyau ba.

Kasar Israyla tace wannan dandano ne tawa kasar Iran zata ci gaba da kai masa hari har sai ta gurgunta shirinta na mallakar makamin kare dangi.

Sojojin Israyla, IDF sun ce suna baiwa kasarsu dama Duniya baki daya kariyane a wannan harin da suka kaiwa Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *