
Dattijon Jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa a yanzu babu dan siyasar dake da karbuwa kamar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace Tinubu bai yi wa Arewa Laifin komai ba.
Yace APC ce ke rike da mafi yawan jihohi kuna ko jihohin da jam’iyyar Adawa ke rike dasu duk sun nuna goyon bayan Tinubu dan haka bai ga me kada shi ba.
Yace amma watakila abubuwa na iya canjawa inda yace amma maganar gaskiya a yanda ake tafiya bai ga wani abu da zai hana Tinubu zarcewa a shekarar 2027 ba.