Tuesday, April 29
Shadow

An kaiwa Tawagar Hadimar Gwamnan Kaduna hari

Hadimar gwamnan jihar Kaduna dake bashi shawara akan harkokin siyasa, Hon. Rachael Averik ta tsallake rijiya da baya a yunkurin kisheta da aka yi.

An kaiwa tawagar Hon. Rachael Averik harin kwantan baunane ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu.

Harin ya farune a tsakanin kauyukan Tsauni Majidadi da Gani dake karamar hukumar Sanga ta jihar.

A ranar tana kan hanyar zuwa Gwantu ne abin ya faru.

A ranar taje gaisuwane sannan ta kaddamar da Asibitin da Alhaji Muhammad Umar Numbu ya gina a masarautar Arak.

Jami’an tsaron dake tare da ita sun budewa maharan wuta inda anan aka jikkata direbanta da Dansanda daya.

Jami’an tsaro a jihar sun fara bincike kan lamarin.

Karanta Wannan  El-Rufai ne ya sani, Inji tsohon Kwamishina a Gwamnatin Jihr Kaduna Bashir Sa'idu da aka kama sa satar kudi

Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *