
Gwamnan rikon kwarya na jihar River, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (retd.) Ya bayyana kin amincewa da binciken da majalisar jihar ke son yi masa.
Ya bayyana hakane bayan da majalisar jihar ta amince ta binciki watanni shida da yayi yana matsayin gwamnan jihar.
A ta bakin me magana da yawunsa, Hector Igbikiowubu, Ibas yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya nadashi kuma majalisar tarayya ta rika lura da aikin da yake.
Yace idan dai majalisar tace zata bincikeshi to tana son ta binciki shugaban kasar kenan da majalisar tarayya.
Saidai yace ba bu wanda zai hana majalisar jihar binciken idan tace tana son ta yi.