
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party a zaben shakerar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, masu hadashi da tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha makiyansa ne.
Peter Obi yace bashi da wata alaka da Abacha.
Yace haduwar da suka yi da Abacha, sun jene a kungiyance a matsayin ‘yan kasuwa masu shigo da kaya daga wajen Najeriya.
Yace amma ba harkar siyasa ce ta hadashi da Abacha ba.
Yace masu yada cewa, yana da alaka da Abacha suna da wata manufa da suke son cimmawa.