Monday, April 21
Shadow

Majalisar Kula Da sarautun Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

Majalisar Kula Da Cibiyoyin Gargajiya A Nijeriya Ta Nuna Damuwa Kan Gayyatar Da Aka Yi Wa Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II

Ƙungiyar ta yi nuni da cewa tuni rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan lamarin, wanda hakan ya sa gayyatar ‘yan sandan bai zama dole ba.

Ƙungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun ko-odinetan ta na ƙasa Alhaji Yahaya Nda Musa, ta bayyana mamakin gayyatar da ‘yan sandan suka yi mai dauke da kwanan watan Afrilu 4, 2025, mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sanda Olajide Rufus Ibitoye, a madadin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda mai kula da sashen leken asiri na rundunar.

Karanta Wannan  Talauci alamace ta yawan zunubi da rashin tsoron Allah>>Inji Pasto Komayya

“Muna da ra’ayin cewa wannan gayyata da babbar hukumar ‘yan sanda ta yi wa Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu cin mutunci ne ga cibiyarmu ta gargajiya, wadda mai kula da ita Sarki ne, don haka muna kira ga ‘yan sanda da su guji yin amfani da wasu masu son kai, waɗanda sana’arsu ke haifar da matsala, da kuma tada zaune tsaye a Kano.”

wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Nigerian cewa tun da farko babban sifeton ‘yan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya kama Sarkin.

Sai dai kuma majiyoyin sun ce Kwamishinan ya bayyanawa Sufeto Janar ɗin cewa, lamarin ba shi da alaƙa da ƙin yin hawan Sallah, kuma Sarkin bai yi amfani da dawakai wajen ziyartar gidan gwamnati ba kamar yadda al’adar ta tanada.

Karanta Wannan  Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga ta hanyar karbar kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 14

Watakila IGP bai gamsu da bayanin da Kwamishinan ya yi masa ba, sai ya umurci sashen binciken asiri na rundunar da ya gayyaci Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *