
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga daga kudaden ruwa da suke karba a hannun wadanda suka baiwa bashi da suka kai Naira Tiriliyan 14.26.
Hakan ya bayyana ne bayan kammala kididdigar da aka yi ta kudaden shigan bankunan a shekarar 2024.
Bankunan da suka samu wadannan kudaden shigar sune, Fidelity, UBA, GT Bank, First Bank, Wema Bank, Stanbic IBTC, FCMB, Access, da Zenith Bank.
Rahoton yace a shekarar 2023 bankunan sun samu kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 6.49 wanda idan aka hada da kudaden ruwan da suka samu a shekarar 2024 na Tiriliyan 14.26, hakan na nufin sun samu karin kaso 119.55 cikin dari kenan na kudin ruwan.
Saidai a gefe guda, yayin da bankunan ke murnar samun kudin ruwa daga hannun wadanda suka baiwa bashin, su kuma wadanda suka karbi bashi a bankunan kokawa suke da tafka Asara.