Sunday, October 25
Shadow

Kalli Bidiyon tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yana fadin cewa Gwamnatin Tarayya tana Baiwa tshàgyèràn Dhàjì kudi da kayan Abinci, inda yayi zargin cewa Jihar Kaduna Biliyan 1 ta basu

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa hanyar da Gwamnatin yanzu ta dauka itace ta baiwa tsageran Daji kudi da kayan abinci wai dan a rika lallabasu kada su rika kai hare-hare kan al-umma.

Yace jihohi da yawa na Arewa na kan wannan tsarin ciki hadda jihar Kaduna.

Malam ya kara da cewa a jihar Kaduna Naira Biliyan 1 aka baiwa tsageran dajin.

Yace suna da hujjoji akan hakan kuma idan lokaci yayi zasu fitar dasu.

Malam ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

https://twitter.com/OurFavOnlineDoc/status/1992320400940990504?t=XMHE9ZcFNCFV6pbOc6vpfA&s=19
Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Malam Abuja ba Kano bace, Wike ya gayawa Sanata Ali Ndume bayan da yacewa Wike ya daina korar Almajirai da sauran masu yawo a Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *