
Rahotanni sun bayyana cewa, Barayi sun sace mashina 3 a wani masallaci dake Tipper garage dake Kuje, babban Birnin tarayya, Abuja.
Lamarin ya farune ranar Asabar a yayin da ake sallar Taraweeh a wani masallaci dake cikin Gidan mai.
Wani shaida me suna Ibrahim Jamilu ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewa, bayan sun kammala sallah, mutane 3 sun bayyana cewa, an sace musu mashina.
Yace sun sanar da kungiyar masu mashina da kungiyar ‘yan Kato da Gora wanda aka bazama neman mashinan.
Saidai ‘yansandan dake yankin sunce ba’a sanar dasu ba.