
Bashin da ake bin Nijeriya ya haura zuwa tiriliyan N144.67 a 2024 – Rahoton DMO
Ofishin kula da basussuka na Nijeriya ya ce bashin da ake bin Najeriya ya karu da naira tiriliyan N47.32tn, wanda ya nuna karuwar kashi 48.58 cikin 100 daga Disamba 2023 zuwa Disamba 2024.
Sabon rahoton da aka fitar a wannan Juma’a, ya nuna cewa an samu karuwar cin bashi daga kasashen waje da kuma cikin gida, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.