
Babban Malamin kirista, Pastor Enoch Adeboye ya bayyana cewa, an masa wahayi cewa, nan gaba a saman wata za’a je a gudanar da taron cocinsa.
Faston ya bayyanawa mabiyansa hakane yayin da yake musu wa’azi.
Saidai yace lamarin Allah akwai ban mamaki amma ba lalai bane sai mutane sun yarda ba.
Lamarin dai ya baiwa mutane da yawa, ciki hadda kiristoci mamaki.