Friday, December 5
Shadow

Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa Naira Tiriliyan N149.39tn

Rahotanni sun bayyana cewa, bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa Naira Tiriliyan N149.39tn.

An tattaro bayanan yawan bashin da ake bin Najeriya har zuwa watan March 31, 2025 inda daga nan ne aka samu wadannan bayanai.

A shekarar data gabata, 2024 dai yawan bashin da ake bin Najeriya Naira Tiriliyan N121.67tn ne wanda hakan ke nufin a yanzu bashin ya karu da Naira Tiriliyan N27.72tn ko ace da kaso 22.8 cikin 100.

Ofishin dake kula da bashin da Najeriya ke ciyowa DMO ne ya fitar da wadannan bayanai ranar Juma’a.

Yawan bashin da ake bin Najeriya na karuwa ne saboda kara cin bashin da gwamnatin tarayya take da kuma faduwar darajar Naira da sauransu.

Karanta Wannan  Dangote ya bayyana jihohin da zai fara kai dakon man fetur kyauta da motocin tankokinsa

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai na dogaro da bashi dan gudanar da ayyukanta, kuma tana cin bashin ne daga cikin gida Najeriya da kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *