Wednesday, November 19
Shadow

Kalli yanda uwa ke zane diyarta saboda diyar tawa uwar kwacen saurayi

Fada saboda saurayi ya zama ruwan dare musamman tsakanin dalibai ‘yan mata a makarantun jami’a.

Ko da a farkon watannan na Yuni da muke ciki, sai da aka ga wani Bidiyo yanda aka ci zarafin wata budurwa, ‘yan mata da yawa suka taru akanta suna duka saboda saurayi.

Abin takaici shine yanda aka dauki Bidiyon faruwar lamarin aka watsa shi a kafafen sada zumunta kowa yaga irin abinda akawa budurwar.

Lamarin ya farune a jihar Ogun, kuma kawayen budurwar sun bayyana cewa da sanin mahaifiyarsu suka aikata wannan danyen aiki dan haka basa shakkar wani ya gani.

Tuni dai hukumar ‘yansandan jihar ta sanar da fara binciken kan lamarin.

Karanta Wannan  Zaɓen cike gurbi: Shugaban karamar hukumar Municipal a jihar Kano kenan, Salim Hashim, ya ke dafa taliyar indomie domin karin kumallo ga ƴan jam'iyyar NNPP da ke garin Shanono don gudanar da zaben cike gurbi

Saidai ko da an hukunta wadanda sukawa wannan Budurwa wannan cin zarafi, ba za’a iya goge tozarcin da suka mata ba.

Uwa na dukan ‘yarta saboda zata mata kwacen Saurayi

Wani abin mamaki da shima ya faru shine yanda aka ga wata uwa a dakin Otal da diyarta, tana dukan diyartata tana cewa zata mata kwacen saurayi.

An ga uwar na daga bulala tana zane diyar inda wani mutum ya shiga tsakani yake kokarin raba fadan.

Hakanan an ji diyar na fadin Mama ban yi niyyar yi miki kwacen saurayi ba.

Wani mutum da dakinsa ke gefan dakin da lamarin ya farune ya dauki Bidiyon faruwar lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Habiba tace Duniya ba wanda take so sai Oga Sani bayan da ta ga Zqrmqlulunsalq

Bidiyon ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda mutane da yawa suka bayyana mamaki da ganin hakan.

Labarai da yawa irin wannan sun faru a jihohin Najeriya daban-daban wanda masana harkokin yau da kullun suka bayyana a matsayin abin damuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *