
Da alama dai Sanata Natasha Akpoti bata da shirin hakura da maganar zargin nemanta da lalata da sanata Godswill Akpabio yayi ba.
A ci gaba da neman hakkinta, a yanzu ta bayyana a kafar yada labarai ta DW inda a can ma ta bayyana irin zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio.
Sanata Natasha Akpoti a baya dai ta yi irin wannan bayyana a kafar Skynews da BBC.
Hakanan ta je majalisar Dinkin Duniya.
Da alama dai so take sai ta karade duka kafafen yada labarai na Duniya da wannan zargi nata.