Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a sake duba tuhumar cin amanar kasa da akewa kananan yara da aka kai kotu na yunkurin kifar da gwamnatin sa ta hanyar zanga-zanga.
Shugaban yace babban lauyan Gwamnati ya duba lamarin dan bayar da shawara kan abinda ya kamata a yiwa yaran.
Yara kanana guda 32 ne dai aka gabatar a babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin cin amanar kasa saboda sun yi zanga-zangar yunwa.
Yaran dai an gansu cikin yunwa da rashin lafiya da firgici inda wasu daga cikinsu suka rika faduwa a farfajiyar kotun.
Tuni dai aka garzaya da guda 5 asibiti.
Hakanan an ga bidiyon yanda yaran ke rububin biskit da ruwa da aka basu dan su ci a cikin kotun.
Lamarin ya jawo Allah wadai ga gwamnati a ciki da wajen Najeriya.