Friday, December 6
Shadow

Bayan shan suka daga ciki da wajen Najeriya, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a sake duba tuhumar cin amanar kasa da akewa kananan yara da aka kai Kotu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin a sake duba tuhumar cin amanar kasa da akewa kananan yara da aka kai kotu na yunkurin kifar da gwamnatin sa ta hanyar zanga-zanga.

Shugaban yace babban lauyan Gwamnati ya duba lamarin dan bayar da shawara kan abinda ya kamata a yiwa yaran.

Yara kanana guda 32 ne dai aka gabatar a babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin cin amanar kasa saboda sun yi zanga-zangar yunwa.

Yaran dai an gansu cikin yunwa da rashin lafiya da firgici inda wasu daga cikinsu suka rika faduwa a farfajiyar kotun.

Tuni dai aka garzaya da guda 5 asibiti.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Bidiyo: Yanda matasan turawa 50 a kasar Denmark suka shiga addinin Musulunci

Hakanan an ga bidiyon yanda yaran ke rububin biskit da ruwa da aka basu dan su ci a cikin kotun.

Lamarin ya jawo Allah wadai ga gwamnati a ciki da wajen Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *