Friday, December 5
Shadow

Bayani Dalla-Dalla: Karanta Kabakin Alherin da Gwamnatin tarayya zata rikawa iyalin Buhari, Za’a rika biyan A’isha Buhari Naira Dubu dari uku da hamsin duk wata amma daga ranar data sake yin aure shikenan za’a daina biyanta, Ji sauran Abubuwan da za’a musu

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{“transform”:1,”square_fit”:1},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:true,”containsFTESticker”:false}

Bayanai sun fito kan abubuwan da gwamnatin tarayya zata yiwa iyalan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bayan da ya rasu.

Rahoton yace za’a rika biyan matarsa watau Hajiya A’isha Buhari Naira Dubu dari uku da hamsin duk wata.

Sannan bayan wata 3 za’a rika biyan su Naira 250,000 dan kula da bukatunsu da kudin makarantar yara.

Hakanan duk bayan watanni 3 za’a rika ba iyalan nasa Naira 250,000 a matsayin alawus.

Hakanan kuma za’a biya musu kudin kula da lafiyarsu a Najeriya dama kasashen waje.

Za’a basu motoci 2 na gwamnati wanda duk bayan shekaru 4 za’a rika canja musu.

Za’a gina musu gida me dakuna 5 a kowane gari suke so a Najeriya.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tsohon Ministan Ministan shari'a, Abubakar Malami ya bar jam'iyyar APC zuwa ADC

Za’a basu jami’an tsaro 4.

Za’a biya musu kudin zuwa shakatawa zuwa gurare.

Za’a basu ma’aikata na gida dana office.

Za’a basu waya daya ta kiran waya.

A’isha Buhari zata ci gaba da amfana da wadannan abubuwan har sai idan ta sake yin aurene tukuna za’a dakatar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *