
Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Bello El-Rufai tare da Dan wasan kungiyar Real Sociedad, Sadiq Zololo sun sayi kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees.
Kungiyar Kwallon kafa ta Ranchers Bees ta kasance a gasar Premier league ta Najeriya tun daga shekarar 1970.
Da yake magana game da sayen Kungiyar, Sadiq ya bayyana farin ciki da kokarin da suke na dawo da martabar kungiyar.
Sadiq ya bayyana cewa, ya taso tun yana yaro yake son Kungiyar ta Ranchers Bees.