Wednesday, September 23
Shadow

EFCC ta saki Tambuwal bayan tsare shi na kwana guda

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Wasu makusantan Sanatan ne suka tabbatar wa BBC sakin nasa, kuma yanzu haka yana gidansa na Abuja.

A ranar Litinin ne hukumar ta tsare shi a Abuja, bayan amsa gayyata kan zarge-zargen fitar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 189.

Kamun da aka yi masa ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ƴan hamayya, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ƴan jama’iyyar haɗaka ta ADC.

Karanta Wannan  'Yan Najeriya da yawa na zuwa banki dan dakatar da aika musu sakon hadadar kasuwanci watau Alert saboda kudin da bankin ke cire musu yayi yawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *