
Malamin Addinin Islama, Sheikh Abubakar Salihu Zaria a bayyana cewa, wata Sabuwar Fitina ta bullo inda ake ganin miji zai baiwa abokinsa lambar waye matarsa ya nemi yin lalata da ita wai dan a ga ko zata yadda.
Malam Yace addini bai yadda da hakan ba inda yace abinda ya bayyana dashi ake amfani, ba’a son bin diddigi ana neman sai an ga laifin mutum.
Sannan yayi kira ga mata su kare martabar aure.
Malam dai ya yi kiran a daina wannan halayyar.