Bidiyon sojan ruwa, Seaman Haruna wanda matarsa taje Brekete Family tana korafin an daureshi tsawon shekaru 6 ya bayyana inda aka ga yanda yaki bayar da Bindigarsa.
Haruna Sojan ruwane amma sojojin kasa ne suka zo zasu kwace masa bindiga.
Dalilin da yasa kenan yaki amincewa.
A bidiyon an ga yanda yake kokawa da sojojin yayin da suke kokarin kwace masa Bindigar amma yaki.
Daga karshe dai an kwace Bindigar aka kaishi aka daure.