
Tauraron mawakin Hausa, Ali Jita ya bayyana cewa ya samu sakonni bayan fitar da wakarsa ta yabon Uwar gida.
Saidai yace an nemi ya yiwa Amarya itama waka.
Yace wakar dan nishadi ne yayi ta kuma yana neman a zauna lafiya a gidaje.
Yace nan gaba kadan Amare su saurareshi zai musu wakarsu suma.