
Alhaji Bakari Bako wanda akewa taken Sarkin Yakin Ma’aiki ya tsinewa Sheikh Lawal Triumph saboda hadisan da ya karanto na cewa an samu kwarkwata akan Annabi sannan an samu Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na fitsari a tsaye.
Ya bayyana haka a wani Bidiyonsa da aka watsa a kafafen sadarwa inda yace ya kamata a dauki mataki akan Sheikh Lawal Triumph.
Ya kara da cewa, Malam Lawal Triumph ba mutumin kirki bane, inda yayi kira ga mutanen Kano su dauki mataki akansa.
Lamarin Hadisan da Malam Lawal Triumph ya karanto akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na ci gaba da dumama yanayi a Kano.