Saturday, June 27
Shadow

Na ga yanda Manya a gidan yari ke yin Lùwàdì da Kananan yara

Matashi Segun Olowookere wanda aka yankewa hukuncin kisa saboda satar kaza da kwan kazar a jihar Osun amma daga baya gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya yafe masa ya bayyana yanda rayuwar gidan yari ta kasance masa.

Ya bayyana hakane a yayin ganawarsa da wakilin jaridar Punchng.

Segun ya kwashe shekaru 14 a gidan yari kuma tun yana dan shekara 17 aka kaishi gidan yarin.

Daya daga cikin labarin da ya bayar da yace yana damunshi shine yanda manya a gidan yarin ke lalata da kananan yara maza ta hanyar luwadi.

Yace daki daya da ya kamata ace mutane 10 ne zasu kwanta a ciki amma sai a tura mutane 50 a ciki.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon inda Amaechi yake cewa su 'yan siyasar Najeriya sun san da wahalar da talakawa ke ciki amma ba ta damesu ba kuma ba zasu daina satar kudin talakawa ba

Saidai yace a tsawon shekarun da yayi a gidan yari, bai bari yayi zaman banza ba, yayi karatu sannan yayi aiki tare da asibitin dake gidan yarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *