
Dan majalisar Wakilai daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa ya nemi a baiwa ‘yan Najeriya dama su rike makamai dan baiwa Kansu Kariya.
Ya bayyana hakane a farfajiyar majalisar Wakilai inda yace idan jami’an tsaro sun kasa, kamata yayi a baiwa ‘yan Najeriya damar kare kansu.
A baya dai Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Lauya dan fafutuka, Deji Adeyanju, da Janar T.Y Danjuma duk sun nemi a baiwa ‘yan Najeriya damar daukar Makamai dan kare kansu