
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, kudin wutar lantarkin da suke biya a duk shekara ya kai Naira Biliyan 47.
Fadar tace dan haka ba zata iya ci gaba da biyan wadannan kudi bane shiyasa shugaba Tinubu ya amince a saka solar.
Shugaban Hukumar makamashi ta kasa, Mustapha Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma’a.
Yace kuma wannan na kan hanyar kokarin Gwamnati na samar da makamashi wanda baya gurbata Muhalli.