Friday, December 5
Shadow

BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci

BUA ya yabawa Tinubu kan karyewar farashin kayan abinci

Shugaban Kamfanin BUA , Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya ce hangen nesa da shugaba Bola Tinubu ya yi wajen samar da rangwamen haraji kan muhimman kayan abinci a bara ya taimaka wajen karya farashin kayan abinci a Najeriya.

Rabiu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawa da Shugaban Kasa a jiya Alhamis.

“Farashin abinci yana raguwa a Najeriya kuma muna kokarin tallafawa wannan yunkuri.

“Za ku tuna cewa mai girma Shugaban Kasa ya bayar da rangwamen haraji a bara domin a shigo da wasu kayan abinci kamar shinkafa, masara, alkama da dawa cikin ƙasa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Idan Babiana ta fita daga Musulunci laifinkune(Musulman Arewa)>>Inji G-Fresh Al'amin bayan da Babiana ta zargi Musulmai 'yan Arewa da cewa suna amfani da Bidiyon ta da ya fita suna cin zarafinta

“A lokacin, farashin abinci ya yi matuƙar tsada; farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a bara ya kai kusan Naira 100,000, buhun alkama ko gari ya kai Naira 80,000, buhun masara kilo 50 ya kai Naira 60,000, sannan kwali ɗaya na taliya ya kai kusan Naira 20,000,” in ji Rabiu.

Ya ce kamfaninsa ya yi amfani da wannan damar inda suka shigo da kaya kamar alkama, masara da shinkafa.

Ya ƙara da cewa tun da jigilar ta fara zuwa kuma suka fara sarrafa kayan, farashin ya fara faduwa.

“A yau, ina farin cikin sanar da ’yan Najeriya cewa farashin shinkafa ya koma kusan Naira 60,000 daga Naira 100,000 a bara. Gari kuma yana Naira 55,000 a buhu, masara kuwa kusan Naira 30,000.

Karanta Wannan  Nan da watan Disamba farashin kayan masarufi zai sauka>>Inji Masana

“Wannan ya samu ne saboda hangen nesa da basirar Shugaban Kasa wajen gabatar da wannan rangwamen haraji na watanni shida,” in ji Rabiu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *