
Tsohon me magana da yawun tsohon shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, ko da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa irin abincin da talakawa ke ci shima yake ci.
Garba Shehu ya bayyana hakane a wani littafi da ya wallafa wanda ya kunshi irin abinda ya faru a lokacin da yayi aiki a matsayin me magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Garba Yace jim kadan bayan zaman Buhari shugaban kasa, an sanar dashi cewa, an ware Naira Miliyan 10 dan abincin fadar shugaban kasa amma shugaban kasar yaki amincewa da hakan.
Garba yace Buhari ya rika tambayar cewa, ku kalli teburina, menen nike ci da za’a ware Naira Miliyan 10?
Garba yace irin abincin da talaka ke ci, Wake, Tuwo, da koko da kosai da alkama da saransu ne shugaba Buhari shima ke ci a matsayin shugaban kasa a wancan lokacin.