
Tsohon hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya haka ramin da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jefa ‘yan Najeriya ciki.
Ya bayyana hakane a wata ganawa ta musamman da aka yi dashi tun bayan da ya ajiye aikin nasa.
Yace Shugaba Buhari ya taba cewa jiki Magayi yace a yanzu ne ma ya kamata a fadi wannan kalma.
Yace nan da watanni 6 za’a kafa wata tafiya wadda zata jagoranci inda Arewa zata fuskanta.