Friday, July 12
Shadow

Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya

A wani abin ban mamaki, dan kwallon tsakiya na Manchester United, Casemiro ya saka hannun jari a kungiyar Marbella FC ta kasar Sifaniya.

Hakanan bayan zuba hannun jarin, a yanzu ya shiga cikin daraktoci masu gudanarwa na kungiyar.

Akwai dai tantamar ci gaba da zaman Casemiro a Kungiyar Manchester United indaa ake alakantashi da barin kungiyar.

A ranar 3 ga watan Yuni dai an ruwaito cewa, Cristiano Ronaldo ya nemi Casemiro ya koma kungiyar Al nassr su yi wasa tare.

Hakanan akwai kungiyoyin Al ahli dana Alqasidiya da suma ke zawarcin Casemiro.

Karanta Wannan  A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *