Thursday, October 3
Shadow

Amfanin aloe vera a gaban mace

Aloe Vera na da amfani daban-daban a jikin dan Adam Musamman mata.

Daya daga cikin amfanin sa a jikin mace shine yana maganin kaikayin gaba. Macen dake fama da kaikayin gaba, tana iya amfani da man Aloe Vera, ko ruwansa, a samu wanda ba hadi a shafa a farji,da yardar Allah za’a samu sauki.

Hakanan me fama da fitar farin ruwa a gabanta,itama tana iya amfani da Aloe Vera dan magance wannan matsala.

Akwai wani bincike da aka yi dan gano ko Aloe Vera na maganin fitar farin ruwa a gaban mace? An ware mata 9 aka basu Aloe Vera suka rika amfani dashi kuma dukansu sun bayyana cewa sun samu Sauki.

Hakanan a wani bincike da aka yi, An gano cewa idan aka hada Aloe Vera da Gurji(Cucumber) suna sawa gaban mace yayi haske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *