Tuesday, February 24
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon wasannin Barkwancin da aka fito dasu dan tsokanar Ministan Abuja, Nyesom Wike biyo bayan Tirka-Tirkar da yayi da sojan Ruwa

Kalli Bidiyon wasannin Barkwancin da aka fito dasu dan tsokanar Ministan Abuja, Nyesom Wike biyo bayan Tirka-Tirkar da yayi da sojan Ruwa

Duk Labarai
Biyo bayan Tirka-Tirkar data faru tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sojan Ruwa, da ya hanashi shiga wani fili a Abuja, wasu sun rika yin wasannin Barkwanci dan tsokanar Ministan. Kalli Bidiyon wasannin Barkwancin kala-kala. https://twitter.com/PoojaMedia/status/1988549632952058286?t=ccTdSosFTEtPOikVvs0z_w&s=19 https://twitter.com/dammiedammie35/status/1988549108601106647?t=1gJd4DL3a_cKe1GOtSje8A&s=19
Bidiyon Dansandannan ya yadu sosai bayan da yace duk Sojan da ya ke ji shi kwallon Shyege ne ya je yawa ‘yansandan Rundunar ‘Police Special Forces’ rashin kunya yaga yanda zata kare tsakaninsu

Wannan dansandan ya dauki hankula bayan da aka ganshi a wani Bidiyo yana fadin cewa, duk sojan da yake ji da kansa, ya je ya tunkari 'yansandan Rundunar 'Police Special Forces' yaga yanda zata kare tsakaninsu. Hakan na zuwane bayan dambarwar da ta faru tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da wani sojan ruwa. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1988500920787702008?t=CMYjoEZwv6skU3g7NKuZAw&s=19
Dan majalisar Wakilai daga jihar Kano, Hon. Sagir Ibrahim Koki ya bar jam’iyyar NNPP

Dan majalisar Wakilai daga jihar Kano, Hon. Sagir Ibrahim Koki ya bar jam’iyyar NNPP

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai, Hon. Sagir Ibrahim Koki ya bar jam'iyyar NNPP. Ya sanar da hakanne a wata sanarwa da ya fitar ranar 11 ga watan Nuwamba inda yace yana godiya da damar da jam'iyyar ta bashi yayi takara a cikin ta. Saidai yace dalilin na barin jam'iyyar, Rikicin Cikin gidane wanda ya hanashi gudanar da ayyukan wakilci da aka zabeshi akansu. Zuwa yanzu dai bai bayyana jam'iyyar daya koma ba.
Kalli Bidiyon: Malamai ‘yan Izala na yin kira ga matasa ‘yan Izala da su daina Yin Murna akan rasuwar Mahaifiyar Malam Abulfatahi ko cewa tana Whuta

Kalli Bidiyon: Malamai ‘yan Izala na yin kira ga matasa ‘yan Izala da su daina Yin Murna akan rasuwar Mahaifiyar Malam Abulfatahi ko cewa tana Whuta

Duk Labarai
Rasuwar malamin Addinin Islama, Dan Dariqa, Abulfatahi Sani Tijjani ta zo da cece-kuce. Mahaifiyar tasa ta rasu kuma an yi jana'izar ta kamar yanda addinin Addinin Musulunci ya tanada. https://www.tiktok.com/@nasiru.sani89/video/7571482873237277970?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7571482873237277970&source=h5_m&timestamp=1762946754&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7568740291232040721&share_link_id=22e2e33d-6163-4ccc-bb3e-eaa897bc967c&share_app_id=1233&ugbiz_name=...
Da Duminsa: Ministan Abuja, Wike ya hana ma’aikatan Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da sojan ruwa ya yadu

Da Duminsa: Ministan Abuja, Wike ya hana ma’aikatan Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da sojan ruwa ya yadu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya haramta amfani da wayar hannu bayan da Bidiyon rikicinsa da wani soja ya bayyana. A wata sanarwa da aka fitar a ma'aikatar ta kula da babban birnin tarayya Abuja, tace daga ma'aikaci na mataki na 14 zuwa kasa, kada a sake ganin wani ya je wajan aiki da wayarsa. Sahara Reporters tace lamarin ya kawo rudani a ma'aikatar inda da yawan ma'aikatan hukumar abin ya basu mamaki. Tuni dai kungiyoyin fafutuka dana kare hakkin bil'adama suka rika Allah wadai da wannan mataki da kuma fadin cewa dakile fadar albarkacin bakine.
Ta yiwa Dangin Tsohon Mijinta Gargadin kada su rabata da Diyarta a Tiktok, saidai da yawa na tambayar Dangin Tsohon Mijin nata na yin Tiktok ne?

Ta yiwa Dangin Tsohon Mijinta Gargadin kada su rabata da Diyarta a Tiktok, saidai da yawa na tambayar Dangin Tsohon Mijin nata na yin Tiktok ne?

Duk Labarai
Wannan matar ta wallafa Bidiyo inda take yiwa Dangin tsohon Mijinta gargadi a Tiktok cewa su kiyayi kokarin rabata da Diyarta. Saidai da yawa na ganin cewa ba ta hanyar Tiktok ne ba ya dace ta aika da irin wannan sakon ba. https://www.tiktok.com/@694418salma/video/7571400454135926023?_t=ZS-91Kq8Av4yzh&_r=1
Rahotanni sun ce, Donald Trump ya fasa kawowa Najeriya Khari, Takunkumi zai kakaba mata

Rahotanni sun ce, Donald Trump ya fasa kawowa Najeriya Khari, Takunkumi zai kakaba mata

Duk Labarai
Wani dan majalisar kasar Amurka, Bill Huizenga ya bayyana cewa, Shugaban kasarsu, Donald Trump da wuya ya kawowa Najeriya hari. Yace maganar da Trump yayi, ya yi tane cikin bacin rai da damuwar asarar rayukan da ake yi a Najeriya. Yace amma Trump takunkumi ne zai kakabawa kasar da masu mulkarta wanda hakan zai fi kawo hari amfani. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV. Yace Trump ba mutum ne me son tashin hankali ba saboda a baya ya baiwa sulhu da zaman lafiya muhimmanci fiye da tashin hankali dan haka ba zai kawo Hari Najeriya ba.
Zhagin da Wike yawa matashin soja cin fuska ne ga Sojan, dama shugaba Tinubu>>Inji Buratai

Zhagin da Wike yawa matashin soja cin fuska ne ga Sojan, dama shugaba Tinubu>>Inji Buratai

Duk Labarai
Tsohon Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, zagin da Ministan Abuja, Nyesom Wike yawa matashin soja da ya hanashi shiga wani Fili dan ya rusashi cin fuskane. Buratai yace dolene a rika girmamawa da kuma sanya jami'an soji a gaba a kasarnan. Yace tsaro shine ke zuwa farko kuma zagin da Wike yawa matashin sojan cin fuskane da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sojan da hukumar sojojin Najeriya. Buratai yace dolene Wike ya fito ya baiwa matashin sojan hakuri, da shugaba Tinubu, dama Hukumar soji. Yayi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki matakin da ya dace akan lamarin. Wike dai ya zagi wani matashin soja ne da ya hanashi shiga wani fili wanda na sojoji ne dan hana ci gaba da gini a filin, sojan yace an bashi umarnine.
Akwai Hanyoyin Shigowa Najeriya guda 1,978 amma guda 84 ne kawai jami’an tsaro ke gadi>>Majalisar Tarayya ta koka

Akwai Hanyoyin Shigowa Najeriya guda 1,978 amma guda 84 ne kawai jami’an tsaro ke gadi>>Majalisar Tarayya ta koka

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai Hon. Isa Mohammed Anka wanda shine shugaban Kwamitin majalisar wakilai dake kula da iyakokin Najeriya ya koka da cewa akwai hanyoyin Shigowa Najeriya daga kasashen waje guda 1,978 amma guda 84 ne kadai jami'an tsaro ke kula dasu. Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan kaddamar da kwamitin na wucin gadi. Ya kara da cewa, wannan matsalar itace tasa ake samun yawan safarar mutane da miyagun kwayoyi da makamai da sauran abubuwan laifi. Yace abinda yasa Gwamnati bata iya samar da tsaro sosai a wadannan hanyoyin shigowa Najeriya sun hada da karancin kudi, da sarkakkiyar hanyoyin da karancin ma'aikata. Ya jinjinawa jami'an Kwastam, dana Immigration wajan kokarin da suke na kare Najeriya akan iyakoki inda yace akwai bukatar hadin kan sauran jami'an tsaron N...